Connect with us

News

Ƙarin farashin fetur: NLC ta lashi takobin durƙusar da al’amura a 2022

Published

on

FB IMG 16410643231510526 1
Spread the love

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

Kungiyar Kwadago ta Najeriya NLC, ta dage cewa ma’aikata da talakawa ba za su sake amincewa da karin farashin man fetur da gwamnatin kasar ke shirin yi ba.

A sakonsa na barka da arziƙin shigowa sabuwar shekara, shugaban kungiyar ta NLC Ayuba Wabba ya ce har yanzu gwamnati ba ta ja da baya a kan aniyar ta ta ba.

Advertisement

‘’To, kungiyar kwadago ta bayyana matsayinta a kan wannan batu. Mun shaida wa gwamnati a fili cewa ƴan Najeriya sun sha wahala sosai kuma ba za su sake jure irin wannan ba’’ inji shi.

NLC dai ta ce a shirye take ta durƙusar da al’amura cik a Najeriya matsawar gwamnati ta sake bijiro da wannan batu.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *