Connect with us

News

Na Haɗu Da Jaafar Ƙorafi Akan Faifan Dala— Abdullahi Abbas

Published

on

Spread the love

Daga Yasir sani Abdullah

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, ya bayyana cewa gaskiya ne ya haɗu da mawallafin jaridar Intanet ɗin nan, Daily Nigerian, Jaafar Jaafar, a Landan.

Abdullahi Abbas ya yi wa Jaafar Jaafar ƙorafi game da me yasa ya saki fayafayan bidiyo da suka nuna Gwamna Abdullahi Umar Ganduje yana karɓar dalolin Amurka a matsayin cin hanci”, kamar yadda jaridar Intanet, Neptune Prime ta rawaito.

“Na daɗe da Ganduje, kuma ba yadda za a yi wani ya ce zan yaudare shi don na haɗu da Jaafar Jaafar a Landan.

Advertisement

“Na je Landan ne don yin hutu da iyalina sai muka haɗu da mawallafin jaridar Daily Nigerian a wani titi muka tattauna kuma na yi masa ƙorafin abin da ya yi wa jagoranmu. Ya faɗa min gaskiyarsa game da labarin, ya buƙaci mu yi hoto kuma muka yi, wannan shi ne ƙarshen labarin”, in ji Abdullahi Abbas.

Game da ta’aziyyar da Gwamna Ganduje ya kai wa tsohon Gwamna, Rabi’u Musa Kwankwaso bisa rasuwar ƙaninsa, Abdullahi Abbas ya ce :hakan ba wani laifi ba ne saboda lokacin da mahaifin Kwankwaso ya rasu, tsohon Gwamna Kwankwaso yana cikin waɗanda suka raka Ganduje zuwa Ƙaraye da Kwankwaso don yi wa Masarautar Ƙaraye gaisuwa.

“Sakamakon haka, ya kamata a yaba wa Gwamna Ganduje. Kuma ko da sun dawo sun yi sulhu babu wane abu game da haka”.

Advertisement

Har yanzu Abdullahi Abbas yana Kotun Ƙoli bisa ƙarar da ya ɗaukaka game da hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke cewa ba shi ne halattaccen shugaban jam’iyyar APC a Kano ba.

Kotun ta ayyana Ahmad Ɗanzago wanda yake a tsagin tsohon Gwamnan Kano kuma Sanatan Kano ta Tsakiya mai ci, Malam Ibrahim Shekarau, a matsayin halattaccen shugaban APC a jihar ta Kano.

“Mutane su sani cewa har yanzu Ganduje yana ƙara a kotu bisa abin da Jaafar Jaafar ya yi masa. Kuma in shaa Allah kotu za ta ba mu nasara”, Abdullahi Abbas ya ƙara da haka.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *