News
KANO: Dubban Mutane Sun Yi Zanga-Zangar Lumana Kan Rashin Wutar Lantarki Na Tsahon Shekaru 20 A Madobi
A Jihar Kano kimanin mutane dubu biyar daga yankunan Kubaraci da Tsauni Kasuwar Gemu Fulani dake ƙaramar hukumar Madobi sun gudanar da zanga-zangar lumana, domin nuna rashin jin daɗinsu kan rashin wutar lantarki da suka ce sun shafe fiye da shekaru ashirin suna fama da ita.
Masu zanga-zangar sun bayyana cewa duk da kafa turakun lantarki tun a zamanin gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau, har zuwa yanzu ba a kammala aikin ba, lamarin da ya sa yankunansu ke ci gaba da kasancewa cikin duhu, yayin da makwabtansu ke cin gajiyar lantarki.
Harin Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Cente Ya Jefa ’Yan Kasuwa Cikin Fargaba
Sun ce sun sha gabatar da koke ga wakilansu a matakai daban-daban, ciki har da ɗan majalisar tarayya mai wakiltar yankin, Sanatan Kano ta Tsakiya, da kuma ɗan majalisar jiha mai wakiltar Madobi, amma babu wani sakamako mai ma’ana da aka samu.
Haka kuma, mazauna yankunan sun ce sun taba miƙa koken nasu kai tsaye ga Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, lokacin da ya kai ziyara yankin, inda suka roƙi a kawo musu dauki, amma har yanzu matsalar na nan daram.
Daya daga cikin jagororin zanga-zangar, Naziru Tsauni Kubaraci, ya bayyana cewa lokaci ya yi da gwamnati za ta saurari koken al’umma tare da ɗaukar matakin gaggawa domin samar da wutar lantarki ga yankunan da abin ya shafa.
A nasa bangaren, wani matashi, Aliyu Idris Kubaraci, ya yi gargadin cewa idan ba a magance matsalar ba kafin babban zabe mai zuwa, akwai yiwuwar al’ummar yankin su kauracewa kada kuri’a.
Masu zanga-zangar sun jaddada bukatar daukar matakin gaggawa daga mahukunta domin kawo karshen matsalar, wadda suka ce na hana ci gaban tattalin arziki da walwalar rayuwarsu.
