News
Da Ɗumi Ɗumi: Khalifa Muhammadu Sunusi II zai jagoranci gina katafaren cibiyar musulunci na ƙasa da ƙasa (International Islamic Center) a jihar Kogi
Daga kabiru basiru fulatan
Khalifa Muhammadu Sunusi II ya bayyana ƙudurinsa na gina katafaren cibiyar musulunci a jihar Kogi, Khalifa ya bayyana haka ne a jawabinsa na taron maulidi a garin Lokoja, Khalifa yace :
” Tun a jiya wajen cin abincin rana na baiwa gwamnan jihar Kogi takarda na neman izinin mallaka muna fili a jiharsa domin mu gina katafaren cibiyan musulunci na ƙasa da ƙasa, ya cigaba da cewa a da kullum idan muka yi taro irin wannan mukan yi saukokin Alqur’ani ne da addu’oi mu watse ba tare da mu kafa wani abu ba, to yanzu insha Allahu ba zamu rinƙa taro muna watsawa kawai ba sai mun kafa wani abu wanda zai amfani musulmai musamman ‘yan tijjaniyyan dake wurin da ma ƙasa baki ɗaya. Lallai Kogi jiha ce da Allah ya albarkace ta da samun yin suruktaka da maulana Sheikh Sharif Ibrahim Inyass RTA dan haka Kogi jihar Shehu ce.”
Muryar Tijjaniya
✍️ Rayyahi Sani Khalifa
08/01/2022