News
Gwamnan Zamfara, ya ziyarci sojojin da su ka ji raunuka sanye da kayan sojoji, a Zamfara
Daga Yasir sani Abdullah
Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya ziyarci sojojin da su ka samu raunuka a yaƙin da su ke yi da ƴan ta’adda a yau Asabar.
Gwamna Matawalle ya ziyarci sojojin ne a asibiti, sanye da kayan sojoji da rigar tare harsashi.
Bayan ya musu fatan samun sauƙi, gwamnan ya jaddada ƙudurin gwamnatin sa na tallafa musu da kula da lafiyar su.
A jiya ne dai rahotanni su ka baiyana cewa ƴan ta’adda masu fashin daji sun hallaka sama da mutane 150 kuma da dama sun ɓata a wani hari da su ka kai kan wasu ƙauyuka a Zamfara.
-
News4 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News6 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News6 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
