Connect with us

News

Katsina: Sojoji 2 da mahaƙa 7 sun mutu yayin musayar wuta kan dunƙulen gwal mai ƙimar Naira miliyan 70

Published

on

IMG 20220109 WA0023
Spread the love

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

 

Katsina: Sojoji 2 da mahaƙa 7 sun mutu yayin musayar wuta kan dunƙulen gwal mai ƙimar Naira miliyan 70

Advertisement

Sojojin Ƙasa guda 2 da kuma haramtattun mahaƙan ma’adanai masu ɗauke da makamai sun rasu a yayin musayar wuta a kan dunƙulen gwal a ƙauyen Magama, wani ƙauye da ke bodar Jibiya da ke Jihar Katsina.

Jaridar Daily Nigerian Hausa ce kaɗai 5a rawaito cewa rikicin ya afku ne a ranar Laraba da misalin ƙarfe 6 na yamma bayan gano wasu dunƙule-dunƙulen gwal a wani ramin haƙo ma’adanai.

Haramtattun masu haƙar ma’adanan, da adadin su ya kai 40, sai da su ka biya sojojin Naira dubu 500 a kan kowanne rami kafin a bar su su fara haƙo ma’adanai.

Advertisement

“lokacin da sojojin su ka ga cewa mahaƙan sun haƙo wani ƙaton dunƙulen gwal, sai su ka dage cewa sai an raba da su,” in ji wani da rikicin ya ritsa da shi ya kuma tsallake rijiya da baya.

“Amma da mahaƙan su ka dage cewa ba za su raba da sojojin ko ƙara musu kuɗi a kan naira miliyan 5 da su ka biya a kan ramuka 5, sai sojojin su ka fara harbin iska.

“Da su ka razana, sai su ma mahaƙan, da ya ke mutum 27 a cikin su su na da bindigogi, sai suma su ka maida martani, inda a ka fara bata-kashi. A ka kashe sojoji biyu su kuma mahaƙan su ka rasa mutane 7.

Advertisement

“Su kuma jagororin mahaƙan sun samu nasarar tserewa da dunƙulen gwal ɗin da kimar sa ta kai naira miliyan 70,”

A watan Maris ɗin bara ne dai Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya aiyana Jihar Zamfara a matsayin wacce jirage ba za su sake bi ta sararin saman ta ba kuma ya hana duk wasu aiyukan haƙo ma’adanai domin dakile aikin ƴan fashin daji da masu garkuwa da mutane.

Wasu majiyoyi sun shaidawa jaridar nan cewa hana haƙo ma’adanai a Zamfara da gwamnatin Buhari ta yi ya sanya mahaƙan su ka koma wasu yankuna a Jihar Katsina.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *