News
Iyayen yara sunyi watsi kan batun kwana hudu a Makarantun Gwamnati
Daga Muhammad zahraddin
Iyaye da malaman yara sun soki matakin gwamnatin jihar Kaduna na maida kwanakin karatu a mako zuwa kwanaki hudu a makarantun gwamnati a fadin jihar.
A cewar iyaye da malaman da aka zanta da su, sabuwar manufar za ta yi illa ga fasahar daliban.
A ranar Lahadin da ta gabata ne gwamnatin jihar a cikin wata sanarwa da kwamishiniyar ilimi, Halima Lawal ta fitar, ta ce za a gyara jadawalin karatu ta 2021/2022 domin tabbatar da ita tayi daidai da sabon kudirin gwamantin na kwana hudu a sati maimakon kwanaki biyar da ake yi.