News
Babu wani fim da za a kara saki a Youtube ba tare da mun tace shi ba – Afakallah
Daga kabiru basiru fulatan
Hukumar tace fina-finai da dab’i ta jihar Kano ta ce daga yanzu babu wani fim mai dogon zango da za ta bari a dora a shi a shafin Youtube ba tare da an tace shi ba.
Shugaban hukumar, Isma’il Na’abba Afakallah, ya shaida wa BBC cewa, sun dauki matakin ne, sakamakon yadda a ke sakin wasu fina-finai da su ka ci karo da al’adu da addinin mutunen jihar ta Kano.
Ya ce“Mu na magane ne a kan yadda sakin fina-finai ya zama ruwan dare a shafin YouTube, wanda kuma ya ke zama illa ga tarbiyya. kuma dole ne mu dauki mataki a kan harkar nan ta fina-finai da wakoki da abubuwan da su ka shafi dangogin rubuce-rubuce,”. In ji shi.
Afakallah ya kara da cewa matakin da su ka dauka ya hada da duk wani fim mai dogon zango da za a dauka a wasu wurare amma daga bisani a kai jihar ta Kano.
Fim din Makaranta da a ke kokarin sakin sa wanda ya saba da koyarwar al’adar Bahaushe da kuma Islama.