Connect with us

News

BUK ta ƙaddamar da cibiyar koyawa ɗalibai sana’ar ɗinki da kwalliya

Published

on

FB IMG 16420976376714943
Spread the love

 

Shugaban Jami’ar Bayero ta Kano, BUK, Farfesa Sagir Abbas a yau Alhamis ya ƙaddamar da cibiyar a jami’ar.

Jaridar indaranka ta rawaito cewa an kafa cibiyar ne domin koyawa ɗalibai sana’o’in ɗinki da kwalliya domin su dogara da kan su idan sun kammala digirin su.

Advertisement

A cewar Shugaban jami’ar, an ƙirkiro da dabarar kafa cibiyar ne domin a taimakawa ɗalibai su iya sana’ar hannu wacce za su dogara da ita kafin su samu aikin gwamnati.

Farfesa Abbas ya ce in dai ɗaliban za su riƙe sana’ar da muhimmanci, to za ta taimaka musu su riƙa samun kuɗin kashewa kuma su samu aikin yi sabo da yanzu gwamnati ba ta bada isassun guraben aiki ga ɗumbin matasa.

“A yau wata gagarumar nasara na sake samu yayin da jami’ar nan ta samu wani gagarumin aiki na haɓɓaka walwalar ɗalibai ta hanyar koya musu sana’o’i.

Advertisement

“Wannan na zuwa ne watanni 2 bayan da jami’ar ta ƙaddamar da tsarin ɗaukar dalibai aiki, inda ɗalibai 125 su ka samu aikin na wucin-gadi,” in ji Shugaban jami’ar.

Ya ƙara da cewa tuni daliban su ka fara ɗaukar albashi, kuma a bayanan danya samu, su na aiki tuƙuru a wajajen aikin na su.

Ya kuma yi kira ga ɗaliban da su yi amfani da cibiyar koya sana’o’in ta hanyar da ya dace, su kuma maida hankali su koyi sana’o’in, in da ya tabbatar da cewa bayan sun bar jami’ar, za su riƙa tuno ta a makarantar da ta ke koya karatu da sana’a.

Advertisement

Ya kuma ƙara da cewa jami’ar za ta ci gaba da binciko hanyoyin da za a riƙa tallafawa walwalar ɗalibai kafin su kammala karatun su a jami’ar.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *