News
Fetur mallakin al’ummar Neja-Delta ne su kadai, ba’a Abuja yake ba – Cif Ayo
Daga Yasir sani Abdullah
Mukaddashin shugaban kungiyar ra’ayin jama’a ta kabilar Yarabawa, Afenifere, Cif Ayo Adebanjo, ya caccaki kalaman da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya yi na cewa man da ke yankin Neja-Delta na Najeriya ne, inda ya ce albarkatun na al’ummar yankin ne.
Dattijon ya kuma yi mamakin ko tsohon shugaban kasar ya na cewa, Allah ne ya halicci albarkatun Neja-Delta lokacin da Najeriya ta kafu a shekarar 1914.
Obasanjo ya bayyana hakan ne a cikin wani rahoto da jaridu ta fitar inda ya ce, man da ke yankin Neja Delta na Najeriya ne, kuma yunkurin da Cif Edwin Clark ya yi na ganin an daidaita lamarin ya ci tura bayan sanarwar da Areas Consultative Forum (ACF) ke goyon bayan matsayin tsohon shugaban kasar.
Cif Adebanjo ya tabbatar da hakan ne a ranar Larabar a wani taron manema labarai da ya gudana a gidansa da ke Legas, wanda ya samu halartar sauran shugabannin kungiyar Afenifere da suka hada da Sanata Femi Okurounmu, Cif Supo Shonibare, Farfesa Ebun Sonaya, Cif Tunde Onakoya, Cif Lanre Anjolaiya, Alhaji Abdullahi Adebayo. Inaolaji, Ms Nike Olujemibola da Jare Ajayi, mai magana da yawun kungiyar ta Afenifere
Shugaban na Afenifere ya bada misali da kundin tsarin mulki na 1960 da 1963 wanda ya tabo batun rabon kudaden shiga wanda a halin yanzu ake kiransa da kula da albarkatun kasa, yana mai cewa kundin tsarin mulkin 1963 ya bada damar biyan kashi 50 cikin 100 a sashe na 140, zuwa yankin da aka samu kudaden shiga.