Connect with us

News

A Najeriya Majalisar dokokin ƙasar na shirin janye batun zaɓen ƴan tinƙe

Published

on

FB IMG 16425696744358751
Spread the love

Daga muhammad muhammad zahraddin

Ranar Larabar nan ne ake sa ran Majalisun Najeriya za su zauna domin sake nazari kan ƙudurin dokar zaɓen da shugaba Muhammadu Buhari ya mayar musu, bayan ya ƙi sa hannu, saboda ba su bai wa jam`iyyun siyasa zaɓi game da zaɓen fid da gwani ba.

Ƴan majalisar sun ce ƙudurin dokar na ƙunshe da muhimman batutuwa masu yawa, saboda haka ba za su bari a yi watsi da shi a kan wani batu guda ɗaya ba.

Advertisement

A baya dai sun yi barazanar cewa za su yi gaban kansu wajen zartar da ƙudurin ya zama doka matuƙar shugaban ƙasar ya ƙi sa hannu.

Shugaban kwamitin kula da hukumar zaɓe na Majalisar Dattawan Najeriya Sanata Kabiru Ibrahin Gaya ya shaida wa BBC cewa a zaman majalisar da za su yi za a tattauna a kan batun da ya sa shugaban ƙasar ya ƙi sanya hannu a kan ƙudurin. Ɗan Majalisar Dattijan ya ce a zaman na su zasu duba batun ba wa jam’iyyu damarsu da shugaban Buhari ya ce ba bu a cikin dokar, sannan a tattauna domin a samu maslaha.

Kabiru Gaya ya ce ”Dama dai kowa ya sani batun da ke da sarƙaƙiya a cikin ƙunshin dokar shi ne batun zaɓen ƴar tinƙe, to a yanzu halin da majalisar ke ciki shi ne wadanda suka dauki abun da zafi a cikinmu sun fara sakkowa, don haka akwai yiwuwar idan suka zauna suka tattauna za a iya samun maslaha a kan batun”

Advertisement

Sanatan ya ce” Dole ne a samu maslaha kan batun zaɓen ‘yar tinke tsakanin gwamnati da majalisar, domin muna so ayi sauri a sanya wa dokar hannu. don idan an barta ba a sanya hannu ba to ko shakka ba bu zaben 2023 zai fuskanci matsala mai yawa”

“Mu abin da za mu yi a matsayinmu na kwamitin kula da hukumar zaɓe a majalisar dattawa shi ne zamu dawo dawo da kudurin dokar zaben a sake tattaunawa a kanta”.

Dama batun zaɓen fid da gwani ta hanyar ‘yar tinƙe, shi ne babban abin da ya janyo taƙaddama a gyaran-fuskar da aka yi wa dokar zaɓen.

Advertisement

Tun da farko wasu daga cikin ‘yan majalisar sun sha alwashin aiki da ikon da kundin tsarin mulkin kasar ya ba su, na tabbatar da dokar ko da shugaban bai sa mata hannu ba.

Wasu na zargin gwamnonin Najeriyar da kai komo fadar Shugaban kasar don ganin cewa Shugaba Muhammadu Buhari bai amince da garambawul din ba.

Masu sharhin siyasa na ganin cewa kin saka hannu da Shugaban kasar ya yi mataki ne da zai yi wa gwamnonin dadi, don ana zargin cewa da dama daga cikinsu ba sa goyon bayan zaben ‘yar tinke wurin tsayar da ‘yan takara a jihohinsu.

Advertisement

A daya bangaren kuma ‘yan majalisa na ganin zaben ‘yar tinken hanya ce da za ta kawo wa gwamnonin cikas, a babakeren da ake ganin suna yi wurin tsayar da ‘yan takara.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *