Connect with us

News

Babu maganar cire tallafin man fetur a yanzu, in ji Lawan bayan ya yi ganawar sirri da Buhari

Published

on

Spread the love

Daga Yasir sani Abdullah

 

 

Advertisement

Shugaban Majalisar Dattijai, Ahmed Lawan ya tabbatar da cewa babu maganar cire tallafin man fetur a halin yanzu kamar yadda jaridu su ka riƙa yayata wa.

Lawan ya baiyana hakan ne yayin da ya ke amsa tambayoyi da ga manema labarai na fadar shugaban ƙasa, jim kaɗan bayan ganawar sirri da Ahugaban Kasa Muhammadu Buhari a Abuja a jiya Talata.

A cewar sa, Buhari bai sahalewa kowa ya cire tallafin man fetur ba kamar yadda wasu su ke jita-jita.

Advertisement

“Ya kamata ƴan ƙasa su ji abinda mu ka tattauna da shugaban ƙasa. Da yawan mu mun damu da bore da zanga-zangar da su ka faru a kwanan nan.

“Hakazalika al’ummar kasar nan a dame su ke. Al’ummomin mu na mazaɓu duk suna cikin damuwa cewa za a cire man tallafin man fetur.

“Dole hankalin mu ya kai kan hakan a matsayin mu na wakilan al’umma kuma masu yin doka.

Advertisement

“Dawowar mu kenan da ga hutu, inda mu ka je cikin al’ummar mu mu ka ji ta bakin su. Mun ji koken su mun kuma fahimci samuwar su. Shi ya sa na ce zan gana da shugaban ƙasa a kan wannan batu da ya sanyawa yan kasa damuwa kuma ya tabbatar min da cewa shugaban kasa ya ce shi bai taba baiwa kowa umarnin cire tallafin man fetur ba,”

Lawan ya yi nuni da cewa duk da tallafin man fetur ɗin nauyi ne a kan gwamnati, to bai kamata a dora shi a kan talakawa ba.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *