News
Da ƊUMI-ƊUMI- Kotu ta umarci Rundunar Sojin Ƙasa da ta baiwa Nnamdi Kanu Naira biliyan 1
Daga kabiru basiru fulatan
Wata Babbar Kotu da ke zaman ta a Umuahia ta baiwa Gwamnatin Taraiya da Rundunar Sojin Ƙasa da su baiwa Jagoran masu Rajin Samar da Yankin Biyafara, Nnamdi Kanu Naira biliyan 1 sakamakon kutsa kai cikin gidan sa a watan Satumbar 2017.
Haka-zalika kotun ta umarci Gwamnatin Taraiya da Rundunar Sojin Ƙasa da su baiwa Kani ɗin haƙuri sakamakon xin zarafin ƴancin shi da su ka yi.
Mai Shari’a, Benson Anya ne ya yanke hukuncin kan ƙarar da Kanu ya shigar ya na tuhumar Gwamnatin Taraiya, Rundunar Sojin Ƙasa da wasu da a ka haɗa a cikin kundin ƙarar.
Ƙarin bayani na nan tafe…