Hukumar sadarwa ta Najeriya ta yi gargadi ga masu amfani da caja ko kuma wajen jona caji a ko ina cewa za a iya yi musu kuste a ko wanne lokaci.
Hukumar ta yi gargadin cewa mutane su daina an sar caja suna sanya wa wayoyinsu daga mutanan da ba su sani ba.
Hukumar ta yi wannan gargadi ne a wani mataki na ba da shawara a karon farko, kan wasu sabbin hanyoyi biyu na kutse cikin waya da suka bullo, daya ita ce ta amfani da caja ko kuma soket dayar kuma ta amincewa da abota a shafin Facebook da ake turawa masu wayar Android.
Sanarwar da aka saki a ranar Juma’a ta ce, nau’in amfani da caja shi ne wanda za a iya arawa mutum caja ya jona daga nan sai a samu damar yin kutse cikin wayarsa har da manhajarsa ta banki, kuma a kan iya yi wa ko wacce irin waya.
Ta kara da cewa nau’in da ake aika abota ta tsarin wayar Android a Facebook shi kuma masu irin wannan wayar kawai ake nufa da irin kutsen.
A mafi yawan lokuta masu wuraren cin abinci ko kanti ko kuma tashohin jirgi akan samar da wuraren caji domin kyautatawa abokan hulda, sai dai a yanzu in ji NCC abin ka iya zamarwa mutane hadari.