Connect with us

Sports

Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Haaland da Rice da Ruiz da Botman da Carvalho da Dembele da Gil

Published

on

123086026 694f17f0 c269 40a4 99b9 ccb36f16ef43.jpg
Spread the love

Daga

muhammad muhammad zahraddin

Manchester City “za ta yi iya yinta” wajen shawo kan ɗan wasan Borussia Dortmund Erling Braut Haaland ya cimma yarjejeniya da su, duk da sanin cewa ɗan wasan asalin Norway zai fi son ya koma Real Madrid. (Athletic, subscription required)

Advertisement

Haaland mai shekara 21, ko da yake baya cikin ‘yan wasan da Real Madrid ke zawarci a yanzu, domin hankalinta ya koma kan ɗan wasan Faransa Kylian Mbappe da ke taka leda a Paris St-Germain. (El Chiringuito, via AS in Spanish)

Ɗan wasan Serbia Dusan Vlahovic mai shekara 22, ya ce bai yi dogon nazari ba wajen kin amincewa da tayin Arsenal da zabin koma wa Juventus a kasuwar ‘yan ƙwallon Janairu. (Metro)

Declan Rice da ke buga tsakiya a West Ham da dan wasan Sevilla Jules Kounde da kuma Aurelien Tchouameni da suke buga wasa tare ɗan Monaco, na cikin wadanda kocin Chelsea Thomas Tuchel ke hari a yanzu. (Athletic, subscription required)

Advertisement

Newcastle United ta gabatar da tayin £40m kan dan wasan Napoli Fabian Ruiz, sai dai bata yi nasara ba, amma tana sa ran sake gwada sa’arta nan gaba. Akwai kuma rahotanni da ke cewArsenal ta kwadaitu da ɗan wasan. (Corriere dello Sport – in Italian)

KocinNewcastle Eddie Howe zai sake koma wa farautar Sven Botman, ɗan shekara 22, bayan rashin sa’a a hannun Lille da ta saye shi kan £35m. (Mirror)

Liverpool na da ƙwarin-gwiwar cewa za ta daidaita da ɗan wasan Fulham mai shekara 19 Fabio Carvalho. (Sky Sports)

Advertisement

West Ham ta gaza dauko aron ɗan wasan Colombia Duvan Zapata daga kungiyarsa ta Italiya Atalanta. (Sky Sports)

ShugabanBarcelona Joan Laporta na da yaƙinin cewa ɗan wasan Faransa Ousmane Dembele, tuni ya amince ya sanya hannun komawa wata kungiya idan kwantiraginsa ya kare a Nou Camp a karshen kakar. (Goal)

Akwai rahotanni da ke Barca ta yi niyyar datse kwantiraginsa, wanda hakan zai bai wa kungiyoyi irinsu Chelsea, Tottenham da Paris St-Germain damar sake shiga zawarcinsa. (Express)

Advertisement

Ɗan wasan Sifaniyar Bryan Gil, ya ce iyayensa sun umarce shi daya koma Valencia a matsayin ɗan aro, wata shida da komawarsa Tottenham daga Sevilla kan £21m. (Sun)

Tsohon kocin Jamus Joachim Low ya amince ya karbi aikin horas da kulob din Turkiyya Fenerbahce(Haber Global, in Turkish)

Rahotanni na cewa ɗan wasanNewcastle United Jamal Lewis, mai shekara 24, ya yi watsi da tayin da ya samu daga Stoke da Birmingham City(Football Insider)

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *