News
Nyas ya musanta baiwa Ganduje haƙuri bisa ƙin halartar zikirin Kano
Daga kabiru basiru fulatan
Babban Halifan Tijjaniyya, Sheikh Muhammad Mahi Ibrahim Nyass, ya nisanta kansa da wani talla da a ka buga a jarida, in da wai ya ke nuna nadama kan rashin amsa gaiyatar da Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yi masa ta halartar taron zikirin da gwamnatin ta shirya.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa an buga tallan mai ɗauke da saƙo da ga Sheikh Nyass ɗin ya na baiwa Ganduje haƙuri kan rashin halartar taron a jaridar Daily Trust ta jiya Talata, 1 ga watan Febrairu.
Sai dai kuma wata sanarwa da kakakin Halifan Tijjaniyyan, Sheikh Tijjani Sheikh Sani Auwal ya fitar a yau Laraba, ta ce saƙon ba da ga Sheikh Mahi Nyass ya ke ba kuma bai baiwa kowa izinin ya rubutawa Ganduje wasiƙa a kan lamarin ba.
Ya ce wasikar ma ba a kan sahihiyar takardar da Shehin ya ke rubuta wasiƙa a kai ba ce kuma babu kwanan wata da lamba a kan takardar, inda ya ƙara da cewa sa hannun da a ka yi a kan wasikar ba na Halifa ba ne saboda ba haka yanke sa hannun sa ba.
Kakakin ya ce Shehin ya na kira ga mabiya Tijjaniyya da su kwantar da hankula su kuma zama masu haɗin kai, inda ya ƙara da kiran mabiyan da su zama masu bin sunnar Manzon Allah (SAW).
Ya kuma yi kira ga mabiyan da su riƙa aikata kyawawan aiyukan da Sheikh Ahmadu Tijjani da Sheikh Ibrahim Nyass su ka riƙa yin wa’azi a kai a lokacin suna raye.
Nyass ya kuma yi kira ga mabiya Tijjaniyya a Nijeriya da duniya baki ɗaya da su haɗa kan su kada su bari shaidanu su samu galaba a kan su.