News
Yan sandan Indiya sun kama wani dan Najeriya mai safarar kwayoyi a karo na uku
Daga kabiru basiru fulatan
Rundunar ‘yan sandan Rachakonda ta cafke wasu masu safarar miyagun kwayoyi guda hudu ciki har da wani dan Najeriya mai suna Mark Owolabi.
Rundunar ‘yan sandan ta ce ta kuma gano gram 38 na hodar iblis daga hannun wadanda ake zargin masu safarar miyagun kwayoyi ne a ranar Talata, kamar yadda jaridar Times of India ta ruwaito.
Jami’an tsaro na musamman (SOT) sun kama Owolabi, mai shekaru 41, wanda ya isa Mumbai a shekarar 2012 bisa takardar bizar kasuwanci.
Sauran wayanda aka kama sun hadar da:
T. Harshavardian, mai shekaru 23, D. Pavan Kumar, 21 da kuma G. Swami Prasad, mai shekaru 23, matashi marar aikin yi daga Neredmet, a Gokul Nagar a Neredmet.
Jami’an ‘yan sandan sun kuma kama kudi (kimanin N122,000), babura biyu masu kafa biyu, wayoyin salula hudu da na’urori, wadanda kudinsu ya kai (kimanin Naira miliyan 5) daga hannun wadanda ake tuhumar.
A cewar Rachakonda CP Mahesh Bhagwat, Mark dan Najeriya wanda ya zama mai fataucin miyagun kwayoyi, ya zauna a Hyderabad a ‘yan shekarun da suka gabata. Tun daga 2018, an kama Mark sau uku.
“An saki Mark daga gidan yari a ranar 24 ga Satumba, 2021. Ya sake fara safarar kwayoyi. Yana karbar N56,000 zuwa Naira 84,000 ko wane giram daya na hodar iblis daga abokan ciniki,” in ji Bhagwat.