News
NIGERIA SAI TA GIRGIZA, RANAR DA ‘YAN KUDU MUKA BAYYANA MATSAYAR MU KAN ZABEN 2023 – WIKE
Daga kabiru basiru fulatan
Gwamnan jihar Rivers Nyeson Wike ya ce, duk ranar da al’ummar kudancin kasar nan suka bayyana matsayarsu kan zaben shugaban kasa da za ayi a shekara ta 2023, kasar nan baki daya sai ta girgiza…
A cewar Nyeson Wike batun tattauna wai mulki ya koma kudu ko ya ci gaba da zama a arewa ma rainin wayo ne.
“Ina tabbatar wa ‘yan Nigeria baki daya cewa dole ne mulki ya koma kudu, babu tantama kan wannan”
“Masu surkulle da shafa labari shuni da suke ganin wai za su bamu mukamin mataimakin shugaban kasa, suna bata lokacin su ne domin munfi karfn hakan ” a cewar gwamnan na Rivers.