Opinion
Zabin Allah muke nema – muhammad muhammad zahraddini
Daga yasir sani abdullahi
An bayyana neman zabin Allah a shugabanci shi ne mafita ga rayuwar ‘yan Nigeria, ta cikin wani rubutaccen sako da Habibu Ahmad Paki ya aikowa da shafin “Gaskiya tafi Kobo”, inda yake cewa.
“A shekarar 2015 yan Nigeria mun tsaya tsayin daka mun kafa mun tsare kuma mun raka domin muga an tabbatar mana da abin da muka zaba ba tare da baiwa Allah zabi ba, sai Allah ya barmu da zabinmu yanzu ga zabin namu yana zanemu ɗaya bayan ɗaya.
Sai dai a wannan lokacin makanta irin ta soyayya ta makantar damu hade da kurumcewa bama ji bama gani idan ba Baba Buhari ba, a wannan lokacin bamu nemi zabin Allah ba kuma duk mutumin da zai ce damu Allah ya zaba wanda yafi alkhairi a makiyin Baba Buhari muke kallonsa domin bama ganin wani alkhairi idan ba Buhari ba”
Muhammad ya kara da cewa.
“Sannan shi ma kansa Buharin yana ganin shi kadai ne mafitar Nigeria, musamman maitarsa da kwaɗayinsa da ya nuna tun a shekarar 2003, a tunaninsa iyawarsa gaskiyarsa da kishin kasarsa ne kadai zai kawowa ƙasa mafita, sai dai ya manta mafitar tana hannun mamallakin mafita me bayar da mafita ko ana so ko ba’a so
Tunda muka miƙa wuya ga Buhari a matsayin mafita sai Ubangiji ya jarabcemu da Buhari yabarmu da Buhari, shima Buharin da ya yarda shi kaɗai ne mafita sai Allah ya jarabceshi damu kuma yabarshi damu”.
A karahe ya yi addu’ar neman shugabannin da suke zabin Allah ba zabin jama’a ba.
“Ya Allah mun tuba bamu da tsumi bamu da dabara, bazamu ƙara cewa sai wane ba, ya Allah zabinka muke nema sai wanda kazaba mana ya Allah ka zaba mana shugaba mafi alkhiri”.