News
Cutar Daji (CANCER) Tana Kashe Mutane 700,000 Duk Shekara – WHO
Daga yasir sani abdullahi
Hukumar lafiya ta duniya (WHO), ta ce, cutar sankara wadda aka fi sani da kansa na hallaka mutane dubu ɗari bakwai 700,000 a kowacce shekara.
Daraktan hukumar na shiyyar Afrika Dr. Matshido Moeti ne ya sanar da haka a yayin da ake bikin ranar masu cutar kansa.
Daraktan ya ce ya na samun masu ɗauke da cutar miliyan goma sha ɗaya 11,000,000 a kowacce shekara.