News
Yanzu Yanzu: Hukumar KTSTA Ta hana Motocin Kano Line shiga Jihar Katsina da fasinjoyi
Daga Muhammad Muhammad zahraddini
Hukumar Kula da Zirga-zirga ta Jahar Katsina ta hana Motocin Kano Line shigowa Jahar Katsina gaba ɗaya.
Wannan mataki an ɗauke shi ne a matsayin maida martani, akan shirin Hukumar Kula da Ƙa’idojin Tuki ta Jahar Katsina-KAROTA, na mayar da Tashar Motar zuwa wani wuri na daban ba tare da sanar da’ita ba.
Motocin Kano Line dai sun kasance motocin da suka fi shigowa da matafiya masu yawa a Jahar Katsina, musamman daga Jahar Kano.
Amma a ƴan kwanakin nan, an ga ƙarancin haka, domin da yawa daga cikin matafiya sai dai su tafi wasu Tashoshin su hau motar Kano, mai makon wadda suka saba hawa domin zuwa Kano.
Sai dai a wani jawabin Hukumar Kula da Zirga-zirga ta Jahar Katsina ta fitar, tace ta hana Motocin Kano Line shigowa Jahar Katsina gaba ɗaya.
A cewar Hukumar KTSTA, ta dauki wannan mataki ne domin jan hankali ga shirin Hukumar KAROTA na maida tashar wani wuri ba tare da sanar dasu ba, wanda suke ganin hakan bai dace ba.
Haka zalika, wannan mataki tuni ya fara aiki, domin matafiya da dama na ƙorafi akan rashin wadatattun Motoci na Gwamnati domin jigila dasu.
Ko a zantawar da Jaridar Katsina Post tayi da wani matafiyi mai Suna Usman Nasiru, yace “Nazo da misalin ƙarfe 4:30 domin hawan motar Kano, amma kawai sai suka ce man Motocin basa aiki a yau, sai dai inje wani wuri in hau mota, kuma wannan ne ya sanya, saida na biya Naira 1000 maimakon ɗari 700 da na saba biya”.