News
PDP ta ɗage taron ta na yankin Arewa-Maso-Yamma
Daga yasir sani abdullahi
A yau Juma’a ne Kwamitin Zartaswa na Jam’iyar PDP ya ɗage taron ta na yankin Arewa-Maso-Yamma, wanda ta sa ranar yin shi a gobe Asabar.
Hakan ne kunshe ne a wata sanarwar mai ɗauke da sa hannun Sakataren Tsare-tsare na Ƙasa, Umar Bature.
Ya ce jam’iyar za ta sanar da sabuwar ranar da za ta yi taron nata, inda ya shaidawa Hukumar Zaɓe, ƴan takara da wakilan zaɓe da ma duk masu ruwa da tsaki a cikin sanarwar.
Jaridar indaranka ta gano cewa duk da PDP ɗin ba ta bada dalilin da ya sanya ta ɗage taron ba, ba ya rasa nasaba da dakatarwar da kotu ta yi wa daya da ga cikin ƴan takarar shugabancin jam’iya na shiyyar, Bello Hayatu Gwarzo sakamakon zargin yi wa jam’iya zangon ƙasa.