News
Duk wanda ya bayyana kansa Shugaban APC za’a kamashi – Matawalle
Daga yasir sani abdullahi
GWAMNAN Jihar Zamfara Alhaji Bello Muhammad Matawalle ya bayyana cewa daga yau babu sauran wanda zai kara bayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar APC a Jihar, in ba wanda uwar jam’iyya ta kasa ta mikawa takardar ba su ne shugabanni.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake yi wa shugabannin jam’iyyar jawabi jim kadan bayan da suka karbi takardar shaidar cewa su ne halartattun shugabannin APC a Jihar Zamfara.
“Batun bude wani ofishi da sunan ofishin jam’iyya duk ya kare a Jihar Zamfara, saboda akwai mai bayar da shawara a kan harkokin gidaje zan bashi umarnin cewa duk wanda ya bude wani ofishi a ko’ina ne da sunan ofishin APC to a dauki mataki a kansa kamar yadda shari’a ta tanadar”.