News
Rikicin Ukraine da Rasha: Martanin da shugabannin duniya ke yi ga Putin

Daga muhammad muhammad zahraddin
Manyan ƙasashen yammacin duniya sun yi ta mayar da martani kan kutsen da Rasha ta yi cikin Ukraine, suna zarginta da dawo da yaƙi baya a Turai.
Shugaban Amurka Joe Biden na fargabar kar a samu munanan asarar rayuka ya kuma ce ƙawayen Amurka za su ƙaƙaba wa Rasha takunkumai masu tsanani.
A gabashin Turai kuwa, fargabar na ƙaruwa ne saboda tunanin halin da za a shiga na kwararar ƴan gudun hijira.
Sauran ƙasashen sun haɗa da China, ta ƙi yarda da kalmar kutse da ake ambata sannan ta yi gum da bakinta. Wasu kuma sun fi mayar da hankalinsu ne kan ƴan kasarsu da ke zaune a Ukraine.
Ukraine ta ce Rasha na kai hare-hare babau ƙaƙƙautawa daga kowane ɓangare, amma har yanzu babu wasu bayanai kan irin ɓarnar da aka samu.
Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi magana kan wani aikin soji na musamman kan kawar da sojoji da aƙidar ƴan Nazi ta Hitler daga Ukraine, amma ba a bayyana sauran manyan burikan nasu ba.
Rashin tabbas ɗin da ake ciki bai hana ƙasashen Turai da suke ƙawance ci gaba da nuna fushinsu ba.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce wannan wani lokaci ne da aka samu sauyin al’amura a tarihin Turai.
‘Ɗanɗana kuɗa‘ – Amurka, Birtaniya da Tarayyar Turai
Mafi yawan ƙasashe sun yi magana ne a kan yin tur da kuma alƙawuran saka takunkumai.
Joe Biden ya ce: “Shugaba Putin ya zaɓi ɗaukar matakin yin yaƙi gaba-gaɗi ne wanda zai jawo munanan asarar rayuka da sanya mutane cikin wahala.”
Ya ƙara da cewa Amurka za ta gana da ƙawayenta don sanya takunkuman tattalin arziki a matsayin azabtarwa.
Shugaban hukumar Turai Ursula von der Leyen ya ce Mista Putin za a ɗora wa alhakin mayar da Turai cikin halin yaƙi. Takunkuman za su raunana tattalin arzikin Rasha da ƙoƙarinta na zamanantar da abubuwa.
Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya ce Mr Putin ya zaɓi bin hanyar zubar da jini da yin ɓarna ta hanyar kai “hare-haren tsokana.
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya ce yana tare da abokansa a gabashin Turai, yana mai cewa Mista Putin zai ɗanɗana kuɗarsa kan wannan kuskuren da ya tafka.
Da yake kira kan wani taron Nato na gaggawa, Mr Macron ya nuna goyon bayan ƙasarsa ga Ukraine.
Mataki ne da ƙasashe da dama suka ɗauka, da suka haɗa da Firaminsitan Italiya Mario Draghi, wanda ya kira harin na Rasha da rashin adalci wanda ba shi da hurumi.
Amma akwai matuƙar damuwa kan abin da ka iya faruwa nan gaba.
Wani ministan Jamus ya yi magana kan “yaƙi ya ɓarke a Turai abin da a baya muke tsammanin a labaran tarihi kawai ake jin su”, yayin da Ministar Harkokin CIkin Gida Nancy Faeser, ta ce Jamus za ta taimaka wa maƙwabtanta idan har aka samu tururuwar ƴn gudun hijira.