News
Ganduje Yana Da Laifukan Cin Hanci Da Rashawa Da Yawa Da Zai Amsa – Kwamitin Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa na Buhari

Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje OFR, wanda yai kaurin suna wajen cusa daloli a aljihu, na fuskantar barazanar tuhuma.
Kwamitin ba shugaban kasa shawara kan yaki da cin hanci da rashawa (PACAC) ya ce gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano yana da tambayoyi da dama dangane da almundahana da zai amsa. Inji Rahoton Daily True Hausa
Sakataren zartarwa na kwamitin, Sadiq Radda ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a dakin taro na yaki da cin hanci da rashawa (ACSR) karo na 26 da aka gudanar a Abuja.
Wasu faifan bidiyo da aka dauko a 2018 a asirce sun nuna Ganduje ya na zuba makudan dalolin amurka. Sai dai ya musanta zargin
Koyaya, a cewar Radda, gwamnan “yana da kararraki da yawa da zai amsa yayin da yake kan mulki da ma fiye da haka bayan ya bar ofis”.
Ya kara da cewa ya yi mamakin yadda dan Ganduje ya kai rahoton mahaifiyarsa ga hukumomin yaki da cin hanci da rashawa bisa zargin zamba.