News
2023: Najeriya za ta zauna lafiya a hannuna, in ji Atiku
Daga Mujahedeen dallami garba
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ce Najeriya da ma ƴan Najeriya za su zauna cikin rayuwa mai aminci a hannunsa idan ya zama wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasa na 2023.
Abubakar ya bayyana haka ne a cikin wani faifan murya da ya fitar a taron Kudu-maso-Yamma na Muryar haɗin kan ƙasa da Ci gaba, wanda kungiyar Atiku Kawai Media Group ke gudanarwa, wanda aka gudanar a Cibiyar MUSON, Legas.
Ya ce Najeriya na bukatar ƙwararrun hannaye tare da hazaka, basira da jajirce wada ƙwazo na ƙwararrun matasa maza da mata.
“Ina sane da manyan kalubalen da masu hangen nesa ke fuskanta yayin da suke fafutukar samar da kasa daga dunkulewar al’umma.
“Irin kishi da kaunar da a ke bukata don gyara Najeriya za su bukaci shugaban da ya san al’amuran tarihi da na zamani na zamaninmu.
“Najeriya da kuma ’yan Najeriya za su samu zaman lafiya a hannu na. Kuma tare, za mu iya dakatar da zage-zage tare da yin amfani albarkatunmu don gina kasa mai wadata, “in ji shi.