News
Yan Bindiga Sun Harbe ’Yan Sa-Kai 63 A Kebbi

Daga kabiru basiru fulatan
Akalla ’yan sa-kai 63 ne aka tabbatar ’yan bindiga sun harbe a Jihar Kebbi.
Lamarin ya faru ne bayan ’yan sa-kan sun kaddamar da farautar ’yan bindigar a masarautar Zuru da ke Jihar.
An dai harbe mutanen ne, wadanda tuni aka riga aka yi musu jana’iza, da sanyin safiyar Litinin.
Rahotanni sun ce ’yan bindigar dai sun buya ne a kan bishiyoyi, inda suka yi wa ’yan sa-kan kwanton-bauna.
Daga bisani dai sun bude wa ’yan sa-kan wuta bayan da suka riga suka gama yi musu kawanya.
Matasan da aka hallaka din dai sun fito ne daga kauyuka daban-daban na masarautar ta Zuru.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoton dai, hukumomin a Jihar ba su ce magantu ba a kan harin.
Hakazalika Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira ga jami’an tsaro da su kara kaimi da rubanya kokarinsu domin dakile shirin yan ta’adda tun kafin su kai ga kaddamar da hare-hare.
Buhari ya yi wannann kiran ne yayin da yake nuna bakin ciki kan abun da ya kira da “mummunan kisan gillar da yan bindiga suka yiwa yan sa kai da dama yayin da suka yi masu kwanton bauna akaramar hukumar Sakaba/Wassagu.”
A cewarsa: “Irin wannan babban ta’asar yana da gigitarwa kuma ina son ba yan Najeriya tabbacin cewa zan yi iya bakin kokarina wajen magance wannan mummunan abu da gaske.
Babban damuwata shine barazana ga rayuwa da wadannan gungun makasan ke yi da kuma daukar rai da suke yi ba a bakin komai ba.”
Shugaba Buhari a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Mallam Garba Shehu, ya fitar, ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan da lamarin ya ritsa da su.
Shugaban ya kara da cewa: “Yayin da nake mika ta’aziyyata ga iyalan wadanda aka yiwa wannan zaluncin, bari na yi amfani da wannan damar wajen sake kira ga jami’an tsaronmu da suk kara kaimi da rubanya kokarinsu domin dakile shirin yan ta’addan tun kafin ma su kai hari.