Sports
Birtaniya ta hana sayar da ƙungiyar Chelsea

Daga kabiru basiru fulatan
Gwamnatin Birtaniya ta yi sammaci ga mamallakin kungiyar kwallon kafar Chelsea, Roman Abramovich.
Dama dai hukumomi sun rike tare da hana biloniyan dan kasar Russia yin dukkan wata hada-hada da ‘yan kasar ta Birtaniya, baya ga ƙaƙaba masa takunkumin hana yin tafiye-tafiye.
Firaministan Birtaniya, Boris Johnson ya ce ba za su lamunci dukkan wani da ke goyan bayan ta’asar da shugaban Russia Putin keyi akan al’ummar Ukraine ba.
“takunkumin yau na zama ɗamba na hana masu taimakawa Russia murkushe ‘yan Ukraine. Za mu saka kafar wando guda da masu goyan bayan kisan fararen hula da lalata asibitoci da mamaye kasashe makwabta,” a cewar Boris Johnson.
Sai dai Boris Johnson ya ce Chelsea za ta cigabada buga gasar firimiya karkashin wani lasisi na musamman amma babu Maganar cefanar da ita kamar yanda Roman Abramovich ke son yi.