Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce har yanzu ta kasa shigar da kayan agaji zuwa yankin da aka yi wa kawanya na Mariupol, abin da ya sa ta bukaci bangarori biyun da ke fada – Ukraine da Rasha – da su ba da tabbacin bayar da damar shiga birnin.
Mai magana da yawun kungiyar, Matt Morris ya shaida wa BBC cewa dole a cimma yarjejeniya da bangarorin biyu domin ba da damar kai wa ga dubban mutane da suka makale a birnin da ke tsananin bukatar agaji.
Ya ce hukumar da ke kula da ayyukan jinkai ta duniya na bukatar a bar mutane su bar birnin, kada a turasasa musu.
Ya ce yawancin wadanda ke birnin na zama ne a wuraren fakewa sannan suna fuskantar karantar abinci da ruwan sha dama magunguna.
Ukraine dai na zargin Rasha da tursasa wa dubban fararen-hula komawa wuraren da take iko da su abin da Rasha ta musanta.
