Connect with us

News

Majalisar dattawa ta nemi sojojin Najeriya su yi amfani da kayan yaki a kan ‘yan fashin daji

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan

Majalisar dattawan Najeriya ta bukaci sojojin kasar su yi amfani da kayan yakin da gwamnati ta samar musu wajen yin luguden-wuta a kan maharan da ke addabar al`umma a shiyyar arewa maso yammacin kasar.

`Yan Majalisar sun yi Allah wadai da harin da `yan bindiga suka kai kan wani jirgin kasa da ke kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abuja, suna cewa ya kamata jami`an tsaro su gaggauta daukar matakin murkushe maharan.

Advertisement

Senata Uba Sani wanda shi ne ya gabatar da kudurin ya ce umarnin zai soma aikin ne ba tare da bata lokaci ba.

“Mun ba shugabannin sojoji umarni da suka hada da na kasa da na sama cewa daga yanzu duka abin da ya kamata a yi su yi amfani da na’urar da muka ba su kudi suka saya domin su yi amfani da ita, su bi wadannan ‘yan ta’adda su yi musu luguden-wuta,” in ji shi.

Advertisement

Majalisar ta kuma nuna damuwa a kan yadda hukumomin tsaro suka rage yawan jami’an tsaro a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna. Ta kuma jaddada bukatar ganin cewa an kare rayukan al’ummar kasar kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

“Yau idan ka tashi daga Kaduna za ka zo Abuja ko daga Abuja za ka je Kaduna, sai ka yi tafiyar kilomita daya ba ka ga jami’an tsaro ko daya ba sai daji”, a cewar Senata Sani.

Advertisement

Sai dai wannan ba shi ne karon farko da Majalisar dokokin kasar ta gabatar da kuduri irin wannan ba amma bai yi tasiri ba ko da yake ta ce za ta ci gaba da bibiyar lamura domin tabbatar da cewa kudurin ya yi tasiri tana mai cewa a shirye take ta yi amfani da wata hanya idan jami’an tsaro sun kasa aiwatar da kudurin.

“Mun yanke hukunci za mu sake kawo jami’an tsaro nan majalisar dattawa domin jin dalilan da suka sa ba sa son su yi haka,” in ji Senata Sani.

Advertisement

Senatan ya kuma sake yin kira ga gwamnatin a kan bukatar samar da ‘yan sandan jihohi saboda a cewarsa wannan zai taimaka matuka waean inganta tsaro a yankunan da ‘yan fashin daji suke kai hare-hare.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending