Connect with us

Labarai

Abdullahi Adamu ya kama aiki a matsayin shugaban jami’yar APC na ƙasa

Published

on

Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

 

 

Sabon zaɓaɓɓen Shugaban Jam’iyar APC na Ƙasa, Abdullahi Adamu, da sauran ƴan Kwamitin Zartaswa na jam’iyar, NWC, sun kama aiki a ranar Laraba, bayan an zaɓe su a Babban Taron jam’iyar a ranar 26 ga watan Maris.

Gwamnan Jihar Nassarawa da sauran kusoshin jam’iyar ne su ka raka Adamu ofishinsa a Shelkwatar APC a Abuja domin bikin kama aikin.

A tawogar kuma har da tsohon shugaban jami’yar na riko, Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni.

Advertisement

Buni, yayin da ya ke danƙa wa Adamu ragamar aikin, ya shaida masa cewa akwai jan aiki a gaban jam’iyar yayin da a ke tunkarar zaɓen 2023.

A nashi jawabin, Adamu, wanda ya ke wakiltar Nassarawa ta Yamma a Majalisar Dattijai kafin zabar sa a matsayin shugaban jami’yar, ya ce zai haɗa kai da gwamnatin taraiya wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro.

Da ya ke magana a kan harin jirgin ƙasa na ranar Litinin, Adamu ya ce gwamnati na maida hankali kan Aiyukan ta’addanci.

Jaridar indaranka ta rawaito cewa Adamu shine gwamnan jihar Nassarawa da ga 1999 zuwa 2007.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending