Connect with us

Labarai

Na Gargadi Gwamnatin Tarayya Ta Dena Jigilar Fasinjoji Da Daddare.

Published

on

Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Daga Muslim yunus abdullahi

 

 

Bisa ga alamu ana yar nuna yatsa tsakanin hukumomin gwamnatin tarayya da na jiha game da harin da yan ta’adda suka kai wa jirgin kasa a Kaduna Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ya ce a baya, ya gargadi hukumomin gwamnatin tarayya game da yin tafiye-tafiyen dare a jirgin A bangarensa, ministan sufuri na kasa, Chibuike Amaechi ya ce ya bukaci a samar da kayayyakin tsaro a baya.

Gwamnan Jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai ya bayyana cewa ya yi gargadin a dena yin tafiyar dare da jirgin kasa na Kaduna zuwa Abuja. El-Rufai ya bayyana hakan ne yayin da ya ke magana da wasu wadanda suka tsira daga harin da yan ta’adda suka kai wa jirgin kasan a ranar Litinin 28 ga watan Maris.

El-Rufai ya ce: “Ka sani ko, na fada wa ministan a dena tafiya da jirgin bayan karfe 5 na yamma. Na ce a dena amfani da jirgin na yamma. Domin mun san akwai yiwuwar a kai hari da dare.”

Advertisement

Fasinjan da ya fada wa gwamnan cewa yana aiki da hukumar jiragen kasa na Najeriya, NRC, ya tabbatar da cewa yan ta’addan sun sace mutane da dama.”

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending