Sports
Kasuwar ‘yan kwallo: Makomar Lacazette, Torres, Haaland, Coutinho, Rudiger, Soucek, Muller
Daga Khadija Ibrahim muhmd
Barcelona na son daukan dan gaban Arsenal da Faransa Alexandre Lacazette, mai shekara 30, a bazara lokacin kwantiraginsa ya kare da Gunners. (Sport)
Manchester United ta sake karkato da hankalinta kan dan bayan Villarreal, Pau Torres, mai shekara 25, wanda daman ta tattauna da shi a baya kafin ta sayi Raphael Varane a bara. (90min)
Manchester City tana da kwarin guiwa cewa za ta yi galaba a kan Real Madrid a zawarcin dan gaban Borussia Dortmund da Norway, Erling Braut Haaland mai shekara 21 a bazaran nan. (ESPN)
Newcastle United na son sayen dan wasan tsakiya na Barcelona da Brazil Philippe Coutinho, mai shekara 29, wanda yanzu yake zaman aro a Aston Villa.(Sport)
Arsenal ta dage sosai wajen ganin ta dauko dan wasan gaban Napoli kuma dan Najeriya, Victor Osimhen, mai shekara 23, da kuma dan gaban Inter Milan da Argentina Lautaro Martinez, mai shekara 24. (CBS Sports)
Aston Villa na shirin kashe kudin da ba ta taba kashewa ba a cefanen ‘yan wasa a bazaran nan inda ake ganin za ta kashe sama da fam miliyan 150 wajen sayen sabbin ‘yan wasa. (Football Insider)
Kociyan Chelsea Thomas Tuchel yana da kwarin guiwar cewa kungiyar za ta sasanta da dan bayanta na Jamus Antonio Rudiger mai shekara 29, kan batun sabon kwantiragi. (Goal)
Leeds na gaba-gaba wajen sayen dan wasan tsakiya na RB Salzburg dan Amurka Brenden Aaronson, inda ake shirin tattauna batun dan wasan mai shekara 21, domin tafiyarsa a bazara. (Football Insider)
An dakatar da tattaunawa kan sabon kwantiragin dan wasan tsakiya na West Ham dan kasar Jamhuriyar Czech Tomas Soucek, mai shekara 27, har sai a karshen kaka, duk da sha’awarsa da manyan kungiyoyi da dama na Turai ke yi. (90min)
West Ham da Leeds na daga cikin kungiyoyin da ke son dawo da dan wasan tsakiya na Jamhuriyar Ireland Josh Cullen, mai shekara 25, zuwa Ingila daga kungiyar Anderlecht ta Belgium. (Teamtalk)
Bayern Munich ta fara tattaunawa kan sabon kwantiragi da dan wasanta dan Jamus Thomas Muller, mai shekara 32. (Bild – in German)
