News
“Sallah: An Samu Karin Kudin Mota Daga Abuja Zuwa Kano, Fasinjoji Sun Makale”
Fasinjoji da dama da ke shirin tafiya daga Abuja zuwa Jihar Kano domin gudanar da bikin Ƙaramar Sallah sun koka kan karin kudin mota da kamfanin sufuri na gwamnatin Kano, wato Kano Line, ya yi bazata, lamarin da ya sa wasu daga cikinsu suka kasa tafiya.
Rahotanni sun nuna cewa tun da farko kudin mota daga Kano zuwa Abuja ya kasance naira 8,000. Sai dai bayan tashin farashin man fetur zuwa kusan naira 1,300 kan kowace lita, kamfanin ya ƙara kudin zuwa naira 11,000.
Sai dai yayin da wasu fasinjoji suka isa tashar motar Mararaba da ke Abuja domin biyan sabon kudin, sun yi mamakin jin cewa an sake ƙara kudin zuwa naira 14,000.
Jaridar Biz Point ta ruwaito cewa an ga fasinjoji da dama cikin damuwa da takaici kan karin kudin da suka ce bai zo musu da wani gargadi ba.
Wani fasinja mai suna Mohammed ya shaida Jaridar cewa ya shirya biyan kudin naira 11,000 kafin daga bisani aka sanar da shi cewa kudin ya tashi zuwa naira 14,000.
“Na shirya tafiya Kano domin bikin Sallah, amma sai aka ce kudin mota ya koma naira 14,000. Wannan ya sa na makale a nan,” in ji shi.
Ya kara da cewa karin kudin ya sa dole ya soke shirin tafiyarsa, yana mai cewa mai yiwuwa ya yi bikin Sallah a Abuja.
Ita ma wata fasinja mai suna Aisha ta zargi mahukuntan kamfanin Kano Line da kara kudin tafiya ba tare da wani bayani ba, tare da kira ga gwamnatin jihar Kano ta shiga tsakani
A cewarta, bai dace a rika kara kudin mota sau biyu cikin kankanin lokaci ba, musamman a lokacin da mutane ke shirin tafiya domin bukukuwan Sallah.
Fasinjojin sun kuma bukaci Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da ya sa baki a lamarin tare da umartar kamfanin Kano Line ya sake duba kudin motar domin saukaka wa matafiya.
Sai dai lokacin da aka tuntubi kakakin kamfanin Kano Line domin jin ta bakinsa, ya ce zai yi bincike Kan lamarin.
