Connect with us

Sports

Juventus da Pogba sun amince wa juna, De Ligt zai koma Chelsea

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan 

 

Advertisement

 

Kungiyar Juventus ta kulla yarjejeniyar sake daukan Paul Pogba, dan wasan Faransa mai shekara 29, na tsawon shekara hudu bayan da wa’adin zamansa a Manchester United ya zo karshe. (Sky Sports)

Advertisement

PSG ta nada Galtier a matakin sabon kociyanta

Chelsea na fatan kammala dauko ‘yan wasan baya biyu – Matthijs de Ligt, dan wasan kasar Netherlands mai shekara 22, da dan wasan Manchester City, Nathan Ake, mai shekara 27. (Standard)

Advertisement

Sai dai Bayern Munich ta ce ita da De Light sun cimma wata yarjejeniya amma ba a rubuce ba. (Sport1 in German)

Har yanzu Tottenham na sha’awar dauko Pau Torres, dan wasan baya na kasar Sfaniya da Villareal mai shekara 25 duk da cewa Clement Lenglet mai shekara 27 na kan hanyar zuwa kungiyar daga Barcelona. (Mirror)

Advertisement

Fulham na daf da dauko Manor Solomon, dan wasan Isra’ila mai shekara 22 daga Shakhtar Donetsk. (Athletic – subscription required)

Newcastle ba za ta iya biyan fam miliyan 60 kudin da Bayer Leverkusen ke bukata kan Moussa Diaby, dan wasan kasar Faransa mai shekara 22. (Telegraph – subscription required)

Advertisement

Ana sa ran Brentford za ta tabbatar da sayo Aaron Hickley, dan wasan Scotland mai shekara 20 kan fam miliyan 18.9, daga kungiyar kwallo ta Bologna cikin wannan makon. (Guardian)

Nottingham Forest ta fara tattaunawa da Bayern Munich kan raba Omar Richards, dan wasan baya kuma dan Ingila mai shekara 24 kan fam miliyan 8.5. (Telegraph via Nottingham Post)

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending