Connect with us

News

Hukumar NDLEA ta kama wani fasinja dauke da ƙunshin hodar Iblis 73 daga Brazil

Published

on

Hukumar da ke yaki da masu tu’ammali da miyagun kwayoyi ta Najeriya, NDLEA ta yi kamu mafi girma a filin jirgin sama na Port Harcourt da ke Omagwa tun bayan da aka kafa ta.

Kakakin hukumar Femi banafemi ya fitar da wata sanarwa da ke cewa hukumar ta kama Nnanna Michael mai shekara 39 wanda ya sauka a filin jirgin saman daga kasar Brazil dauke da kunshi 73 na hodar Iblis wanda nauytinsu ya kai kilo 8.15.

Advertisement

An kama shi ne yayin da ake binciken fasinjojin da suka iso Najeriya cikin wani jirgin saman kasar Qatar wanda ya taso daga birnin Doha zuwa Port Harcourt.

An gano kunshin hodar Iblis din ne cikin wasu kayatattun zannuwan gado shida da aka dinke su ciki.

Advertisement

Bayan da aka bincike shi, Mista Nnanna ya ce ya taso daga birnin Sao Paolo na kasar Brazil ne zuwa Qatar san nan ya isa Port Harcourt, kuma ya ce wani mutum ne da bai san sunansa ba ya ba shi sakon zannuwan gadon guda shida domin ya mika wa wani mutumin na daban, wanda shi ma bai san sunansa ba a filin jirgin saman na Port Harcourt.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending