Connect with us

Labarai

Wahalar neman ruwa ke hana yara zuwa makaranta a sassan birnin Kano.

Published

on

Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Daga Kabiru basiru fulatan

 

 

 

A yayin da yanayin zafi ya kankama, jama’a a Jihar Kano sun koka matuka kan yadda suke shan wahala wajen samun ruwan amfani na yau da kullum a ciki da fadin jihar.

Baya ga wahalar da ake sha wajen samun ruwan, jama’ar sun koka sakamakon tsadar da ruwan ya yi, inda a wasu sassan ake siyar da ruwan a kan kudi N70, sabanin N30 da ake siyarwa a baya.

Advertisement

Duk da cewa Kano na da madatsun ruwa masu dimbin yawa, matsalar karancin ruwan sha na ci gaba da ci wa al’ummar birni da kewayen jihar tuwo a kwarya.

Unguwannin da suka fi fama da wananan matsala sun hada da yankin Kurna, Bachirawa, Fagge, Birged, Hotoro, da ma mafi yawan sassan kwaryar birnin Kano.

Hukumomi a jihar dai na cewa suna yin bakin kokarinsu wajen samar da wadatacce sannan kuma tsaftataccen ruwan sha.

Sai dai alamu na nuna akwai jan aiki a gaban hukumomin kasancewar birnin Kano na kara fadada sannan kuma bututun ruwan bai kai wurare da dama ba.

Yara ‘yan makaranta ba sa samun zuwa makaranta ko kuma ba sa zuwa da wuri sakamakon fadi-tashin neman ruwa.

Toh ko yaya matsalar ta ruwa ta ke a yankunan ku?

Advertisement

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending