Labarai
YANZU-YANZU: Malamai 6 sun rasu a kan hanyarsu ta dawowa daga yin da’awa a Kano

Daga kabiru basiru fulatan
Rahotannin da su ke iske mu yanzu-yanzu sun baiyana cewa malamai shida ne su ka rasu a haɗarin mota a kan hanyar su ta dawo wa daga Karamar Hukumar Sumaila, Jihar Kano bayan sun je musuluntar da maguzawa, wato da’awa kenan da harshen larabci.
Wata majiya da ga Imamu Malik Foundation, gidauniyar da a ƙarƙashin ta ne malaman su ke zuwa da’awar, ta ce dukka malamai, shidan waɗanda kuma su ne jagororin da’awar, sun rasu.
A cewar majiyar, a yau da safe ne dai malaman, har ma da wasu ɗaliban su, su ka tafi Sumaila ɗin domin musuluntar da maguzawa.
Sai dai majiyar ta ce ba su samu labarin cewa ɗaliban sun rasu ko sun ji raunuka ba, amma ta tabbatar da cewa malaman duk sun rasu.
Ta ce Mallam Alƙassim Zakariyya, shine jagoran tafiyar, shima ya rasu.
“Yanzu haka muna can Imamu Malik Foundation a unguwar Dakata, muna jiran sauran ɗalibai su karaso sai mu wuce gidan Sheikh Alƙassim Zakariyya, inda a nan ne za a yi musu jana’izar,” in ji majiyar, wacce ta nemi a dakatar sunan ta.
Da mu ka tuntuɓi Kakakin Hukumar Kare Hadarurruka ta Ƙasa, FRSC, a Kano, Abdullahi Labaran ya ce har yanzu dai basu samu labarin ba amma zai bincika.
Ƙarin bayani na nan tafe…
-
Labarai7 days ago
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Yi Wa Masu Digirin Ƙasashen Waje Jarrabawa
-
Labarai3 days ago
Jami’an Tsaro A Pakistan Sun Kama ’Yan Najeriya 20 Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi
-
Labarai2 days ago
Hare-haren Ta’addanci Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 835 A Najeriya Cikin Wata Guda – Rahoto
