Dazu-dazu BBC ta sami rahoto cewa dakarun Ukraine sun harba wasu makamai kan wani babban jirgin ruwan yaki na Rasha mai suna Moskva.
Advertisement
To ma’aikatar tsaron Ukraine ta kara fitar da wani bayani, tana cewa jirgin ya fara nutsewa bayan da makaman Ukraine masu linzami samfurin Neptune suka lalata shi.
Sai dai Rasha ta musanta cewa Ukraine ce ta harbi jirgin ruwan, tana cewa gobara ce ta kama a sanadin wani hadari da ya auku a cikin jirgin.
Advertisement
Ta kuma ce tuni aka kashe gobarar kuma jirgin ruwan na kan hanyarsa ta komawa wata tashar jiragen ruwa a Rasha.
Ga wasu hotunan jirgin na Mosva, wanda ke cikin manyan jiragen yakin kasar da ta ke afahari da shi.
Advertisement
KremlinCopyright: Kremlin
A watan Agustan 2014 Shugaba Putin ya karbi bakuncin Shugaba Abdul Fattah al-Sisi a bisa jirgin ruwan na MoskvaImage caption: A watan Agustan 2014 Shugaba Putin ya karbi bakuncin Shugaba Abdul Fattah al-Sisi a bisa jirgin ruwan na Moskva
A wannan hoton ana iya ganin jirgin ruwan na Moskva yana gwajin wasu makamai masu linzami a watan Afrilun 2021Image caption: A wannan hoton ana iya ganin jirgin ruwan na Moskva yana gwajin wasu makamai masu linzami a watan Afrilun 2021
Maxar TechnologiesCopyright: Maxar Technologies
A nan kuma ga hoton da aka dauka daga tauraron dan Adam da ke nuna jirgin ruwan na Moskva yayin da yake tashar jirgin ruwa na Sevastopol a yankin Crimea