Connect with us

News

Yan sandan Indiya sun damke wani limamin addinin Hindu mai barazanar yi ma mata Musulmi fyade

Published

on

Daga yasir sani abdullahi

 

Yan sanda a arewacin Indiya sun kama wani limamin addinin Hindu mai tsaurin ra’ayi da ake zargi da yin barazanar yi wa mata Musulmi fyade a lokacin da suke gudanar da zanga-zangar addini a jihar Uttar Pradesh.

An tsare Bajrang Muni Das ne sama da kwanaki goma bayan ya yi wadannan kalamai masu tayar da hankali a gaban jami’an ‘yan sanda.

Bidiyonsa yana yayin da yake barazana ga musulman ya karade shafukan sada zumunta, abin da ya janyo masa tofin Allah-tsine.

Ya ba da hakuri kan kalaman nasa bayan ‘yan sanda sun kaddamar da bincike a makon jiya.

Jam’iyyar Hindu-BJP ce ke mulkin jihar.

Advertisement

Kamen dai ya zo ne kwanaki bayan da aka yi arangama tsakanin mabiya addinin Hindu da Musulmi a yayin gudanar da wani jerin gwano da ke da alaka da addini.

Masu fafutuka sun ce an lalata dukiyoyin Musulmi da dama a tashin hankalin.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending