Connect with us

News

Rasha ta gargaɗi Amurka da ƙawayenta kan ba Ukraine makamai

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

Rasha ta yi gargadi Amurka da kawayenta a hukumance kan taimakawa Ukraine da ƙarin makamai.

Sakon na diflomasiya da kafar yaɗa labaran Amurka ta gani – an aike shi ne tun ranar Talata, kafin shugaba Biden ya sanya hannu kan umarnin sake taimakawa Ukraine da makaman da kuɗinsu ya kai dala miliyan 800.

Rasha ta ce makaman da Amurka ke turawa Ukraine na sake rura wutar rikicin, kuma suna iya haifar da mumunan yanayin da kowa zai ɗanɗana koɗarsa.

Wani dan majalisar dokoki a Birtaniya Bob Seely, ya ce yana ganin yanayi zai yi muni matuƙa, sai dai kuma abin diga ayar tambaya shi ne ya ake son Ukraine ta yi?

Kayan yaƙin da Amurka ta tallafawa Ukraine a wannan karon sun hada da makaman artilare da jirage marasa matuka, da na’urorin kakkabe makamai da helikwafta.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending