Connect with us

News

Rasha ta haramta wa Boris Johnson shiga ƙasarta

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan

 

 

 

 

Rasha ta haramta wa Firaministan Birtaniya Boris Johnson shiga ƙasar saboda matsayin da Birtaniya ta ɗauka a yaƙin Ukraine.

Ma’aikatar harakokin wajen Rasha ta ce matakin ya shafi Sakataren harakokin waje Liz Truss da na tsaro Ben Wallace da wasu mambobin gwamnatin Birtaniya 10 da ƴan siyasa.

Advertisement

An dauki matakin ne “saboda matakin nuna ƙiyayya da gwamnatin Birtaniyya ta ɗauka, musamman na sanya takunkumi kan manyan jami’an Rasha”, a cewar sanarwa da ma’aikatar ta fitar, ta kuma ƙara da cewa nan ba da jimawa ba za ta ƙara yawan sunayen.

Tuni Rasha ta haramta wa shugaban Amurka Joe Biden da wasu manyan jami’an Amurka shiga ƙasarta

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending