Connect with us

News

Najeriya kuma ta tura dakarun Soji 205 kasar Gambia domin wanzar da zaman lafiya

Published

on

Daga yasir sani abdullahi

 

 

 

Rundunar sojin Najeriya ta aike da dakaru 205 zuwa kasar Gambia domin gudanar da aikin wanzar da zaman lafiya.

Jawabin Hakan dai ya zo ne a daidai lokacin da ta ke tabbatar da aniyar Najeriya na tura dakaru masu hazaka a wani bangare na kokarin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a fadin duniya.

Advertisement

Da yake jawabi a wurin taron tawagar ECOWAS da ya gudana a dakin taro na Martin Luther Agwai dake Jaji, jihar Kaduna a jiya, babban hafsan soji na hedikwatar sojojin, Manjo-Janar Olufemi Akinjobi, ya ce Najeriya ta samu nasarar shiga ayyukan wanzar da zaman lafiya guda 40 tare da tura dakaru sama da 100,000 tun daga shekarar 1960 zuwa yau.

Akinjobi wanda ya samu wakilcin Manjo-Janar Zakari Abubakar, ya ci gaba da cewa, an kafa tawagar dakarun ECOWAS ne domin zuwa Gambia a matsayin tawagar shiga tsakani domin warware rikicin tsarin mulkin kasar bayan zaben shugaban kasa da aka yi a shekarar 2016, wanda ya ce zai taimaka wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali ta hanyar kwarewa da aikin sojoji.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending