News
Nijar ta ga watan Shawwal, Najeriya kuwa sai Litinin za a yi Sallah
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sanar da ganin watan Shawwal, wanda ya kawo karshen watan azumin Ramadan a kasar.
Tuni dai Shugaba Mohamed Bazoum ya aike da sakon ‘Barka da Sallah’ ga ilahirin al’ummar kasar a shafinsa na Tuwita, inda ya yi addu’ar zaman lafiya da tsaro da hadin-kan kasar.
Wannan na zuwa bayan Najeriya, makwabciyar Nijar, ta sanar da cewa ba a ga watan ba tare da ayyana Litinin a matsayin ranar Sallah.
Kwamitin ba da shawara kan harkokin addini na Majalisar Sarkin Musulmi tare da hadin gwiwar kwamitin ganin wata na kasa ya ce bai samu wani rahoto daga kwamitoci daban-daban na kasar da ke tabbatar da ganin jinjirin watan Shawwal ba.
-
Opinion4 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News2 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
