Connect with us

News

Kisan Kai: Kotu Ta Yanke Wa Matashi Mai Shekaru 19 Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya

Published

on

 

Wata babbar kotu ta yanke ma wani Ibrahim Khalil mai shekaru 19 hukuncin kisa ta hanyar rataya a Kano, sakamakon garkuwa da ]an yayar shi mai shekaru biyar mai suna Ahmad Ado da kuma zama silar mutuwar sa da ya yi.

Advertisement

An dai yanke wa Ibrahim Khalil hukuncin laifuffuka biyu, wa]anda su ka ha]a da garkuwa da mutane da kisan kai.

Alkali Usman Na’abba ya tsaya a kan cewa, masu gabatar da ƙara sun tabbatar da zargin da su ke cike da dalilai masu yanke hanzari, kuma ya yanke ma wanda aka kama da laifin garkuwa da mutanen hukuncin shekaru 14 a gidan maza.

Advertisement

Mai shari’a Na’abba, ya kara da yanke ma shi hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda kama shi da laifin kisan kai da aka yi.

Tun farko dai lauyan masu ƙara Lamido Soron ɗinki, ya sanar da kotu cewa wanda aka yanke wa hukuncin ya aikata laifin a shekara ta 2019 a rukunin gidaje na Karkasara da ke birnin Kano.

Advertisement

A wani labarin kuma Jami’an tsaro sun damke wani mutumi mai suna Kabiru Abdullahi wanda ake zargi da kisan diyar makwabcinsa, Khadija yar shekara biyar a jihar Bauchi.

Kakakin hukumar Civil Defence na jihar, Garkuwa Adamu, ya bayyana hakan a cikin wata samarwa da ya raba wa manema labarai.

Advertisement

Ya yi bayanin cewa an damke Abdullahi ne tare da Alhaji Yawale kan zargin garkuwa da diyar Abdullahi Yusuf a Sabon Gari Narabi a karamar hukumar Toro.

Adamu yace: “Bincike da aka fara sun nuna cewa Kabiru Abdullahi ya sace Khadika a gaban gidansu kuma ya shaketa ya jefata cikin buhu.”

Advertisement

“Sai ya tuntubi mahaifinta Abdullahi Yusuf ya bukaci kudin fansa. Bayan tattaunawa, sun amince kan N150,000 don a saketa.”

A cewar Kakakin NSCDC, Yawale ya karbi N150,000 karkashin bishiyar tsamiya a garin Narabi. Yace: “Bincike ya kara nuna mana cewa an kashe Khadija ranar 27 ga Afrilu, 2022, kuma ya birneta dakin girkin abinci a gidansa.”

Advertisement

“Masu bincike sun hako gawarta kuma sun kai asibitin Toro.”

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending