Labarai
Taba sigari na kashe ‘yan Najeriya 29,000 a kowacce shekara’

Daga kabiru basiru fulatan
Wani mai bincike kan cigaban tattalin arziki a Afirka ya ce taba sigari na sanadin rayukan ‘yan Najeriya 29,000 a kowacce shekara.
AL’AJABI:Duk Da Amfani Da Maganin Hana Daukar Ciki, Mai ’Ya’ya 7 Ta Haifi ’Yan 4
Austin Iraoya da ke aiki da cibiyar tattalin arziki ta Afirka ya ce ‘yan Najeriya na kashe naira biliyan 526 wajen shan sigari da neman maganin cututuka da taba ke haifarwa.
Jaridar Daily Trust a Najeriya ta rawaito, Mista Austin na cewa wannan al’amari na yin mumunan illa ga tattalin arzikin kasa.
Kuma a cewarsa gwamnati na samun harajin kashi 10 cikin 100 ne kacal, na wadannan kuɗaɗe da ake ɓarnatarwa wajen shan sigari.
Waɗannan bayanai nasa na zuwa ne a lokacin bikin ranar yaƙi da shan taba sigari da aka gudanar a birnin Tarayyar Najeriya wato Abuja a jiya Litinin.
-
Labarai6 days ago
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Yi Wa Masu Digirin Ƙasashen Waje Jarrabawa
-
Labarai2 days ago
Jami’an Tsaro A Pakistan Sun Kama ’Yan Najeriya 20 Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi
-
Labarai1 day ago
Hare-haren Ta’addanci Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 835 A Najeriya Cikin Wata Guda – Rahoto
