News
Kungiyoyi kare hakki na bincike kan zargin kisa a zaɓen fitar da gwanin APC a Kano
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Hukumar kare hakkin bil adama ta kasa da haɗin gwiwar kungiyoyin farar-hula a Kano sun kaddamar da kwamitin bincike kan zargin kisan mutane uku a zaɓen fidda gwanin da APC ta gudanar a Kano.
Hajjin 2022: Mun tanadar wa alhazan mu masaukai kusa da Harami – Gwamnatin Katsina
Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta rawaito yadda wani mai takarar gwamna a inuwar jam’iyyar APC, Sha’aban Sharada, ya zargi cewa an kashe magoya bayansa da jikkata da dama a lokacin zaɓen fitar da gwani da aka gudanar ranar Alhamis.
Kwamitin mutane 11 da aka naɗa karkashin jagoranci, Shehu Abdullahi na hukumar kare hakkin bil’adama da Ibrahim Waiya na ƙungiyar farar-hula a Kano.
Waiya ya ce ana saran kwaimitin ya gabatar da rahoton da ya tattara nan da mako uku domin gaggauta bincike.
Sannan an samu wata gamayar kungiyoyin farar-hula a Kano da su ma suka bukaci a soke zaɓen fitar da gwani na APC kan zargin tafka kura-kurai da aringizo.
Mataimakin gwamnan Kano, Nasiru Yusuf Gawuna ne dai ya lashe zaɓen bayan doke abokin takararsa Sha’aban Ibrahim Sharada.
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion7 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News3 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
