Connect with us

News

Gwamnan Zamfara ya sanya hannu kan dokar aiwatar da hukuncin kisa kan muggan laifuka

Published

on

MATAWALLE

Daga kabiru basiru fulatan 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Gwamnan Jihar Zamfara a Najeriya Bello Matawalle ya sanya hannu kan wata doka da za ta hukunta dukkan wadanda hukumomin jihar suka kama suna aikata laifuka kamar na kora shanu, satar mutane da shiga kungiyoyin asiri da kuma aikata ta’addanci.

Advertisement

Ƴan bindiga sun harbe mutum 8 a wajen bikin suna

Tun a jiya Litinin dai majalisar jihar ta mika kudurin dokar bayan wani zama na musaman da dukkan ‘yan majalisar suka halarta.

Advertisement

 

Dokar ta tanadi hukuncin kisa ga dukkan wanda aka samu sun aikata wadannan laifukan.

Advertisement

 

An amince da kudurin dokar ne yayin wani zama da dukkan ‘yan majalisar Jihar Zamfara suka halarta Gusau babban birnin Jihar.

Advertisement

 

Matsalar tsaro a yankin yayi mummunan tasiri ga jama’ar jihar, wadda ta hada da bayyanar ‘yan bindiga da barayin daji da masu satar mutane domin karbar kudin fansa.

Advertisement

 

Hakazalika ana fama da masu sanar da wadannan miyagun mutanen halin da mazauna garuruwa da kauyukan jihar ke ciki domin su kai musu hare-hare.

Advertisement

 

Lamarin ya kai matsayar da tilas jama’a ke kauracewa muhallansu zuwa wasu yankunan domin neman mafaka.

Advertisement

 

Manoma ba sa iya zuwa gonakinsu, kuma wasu kauyukan da garuruwan sun zama tamkar kufai.

Advertisement

 

Wani cikin misalan irin tabarbarewar da al’amura suka yi, a baya-bayan nan, shi ne yadda ‘yan bindiga suka addabi garin Mada, kuma suka tarwatsa mazauna garin duk da cewa yana kusa da Gusau babban birnin jihar ne.

Advertisement

 

Akwai tambayoyi masu dama a zukatan ‘yan Najeriya, musamman kan tasirin da wadannan tagwayen matakan da gwmantin Zamfara ta dauka domin kokarin magance matsalar tsaro – na farko yin kira ga jama’ar jihar da su mallaki makamai domin kare kansu, da kuma kafa wannan dokar da gwamnan jihar ya sanya wa hannu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending