News
Yanzu-yanzu: An ga Watan Babbar Sallah Yau a Saudiyya.
Daga yasir sani Abdullah
A yammacin yau Laraba ne shafin Masallacin Harami na Saudiya ya bada sanarwar ganin jaririn watan Zul-Hijja, haɗe da sanarwar cewa Mahajjata za su yi tsayuwar Arfa a ranar Juma’a 8 ga watan Yuli, 2022.
Zargin safarar sassan jiki: Gwamnatin Nijeriya ta ɗauki lauyoyi domin kare Ekweremadu da matarsa
Hakan na nufin ranar Asabar ta sama wacce tai daidai da 9 ga watan Yuli, 2022 zai kama ranar Salla Babba.
A Najeriya ma a jiya ne Sarkin Musulmi ya bada umarnin a fara duba watan Babbar Sallah ɗin, wanda idan an ganshi yau, za’a yi sallah rana ɗaya da Saudiyya ɗin; wato Asabar ta sama.
Advertisements
