News
Kotu Ta Daure Dan Damfara Shekara 235 A Kurkuku
Daga kabiru basiru fulatan
Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Uyo, babban birnin Jihar Akwa Ibom, ta yanke wa wani mutum da ta samu da laifin damfarar kasa da kasa hukuncin daurin shekara 235 a gidan kaso.
MASU SHAYE SHAYE FIYE DA 500 SUN FECE DAGA GIDAN GYARAN HALI A SRI LANKA
Alkalin kotun, Mai Shari’a Agatha Okeke ce ta yanke hukuncin yayin zaman kotun na ranar Laraba.
Kotun dai ta sami mutumin ne mai suna Scales Olatunji da laifin damfarar kudaden da yawansu ya kai Naira miliyan 525.
An gurfanar da Scales Olatunji ne ranar biyu ga watan Yulin 2019 ana tuhumarsa da laifuka 45 masu alaka da aikata sojan gona, hada baki da kuma zambar kudade.
Sai dai ya musanta aikata laifukan da aka zarge shi da aikatawa.
Advertisements
